Home NewsGwamnatin tarayya ta bayyana cewa kaso 70 cikin dari na kasafin kudin shekarar 2025 za a tsallaka da shi zuwa sabuwar shekarar 2026.

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa kaso 70 cikin dari na kasafin kudin shekarar 2025 za a tsallaka da shi zuwa sabuwar shekarar 2026.

Ministan kudi da tsare-tsaren tattalin arziki na kasa Wale Edun ya bayyana hakan ayayin wata ganawa da kwamitin kudi na majalisar dattawa da kuma mambobin kwamitin tattalin arziki da shugaban kasa ya kafa akan tsare-tsaren kudaden da gwamnati ta ke son kashewa na matsakaicin zango daga shekarar 2026 zuwa 2028.

Ayayin ganawar shugaban Kwamitin kudi na majalisar Dattawa Sanata Sani Musa, ya ce zaman tattaunawar na da nasaba da bukatar bangaren zartaswa zuwa ga shugaban majalisar dattawa Godswil Akpqbio na neman amincewar Majalisa akan tsare-tsaren kasafin kudi na matsakaicin zango daga shekarar 2026 zuwa 2028 wanda majalisar zartaswa ta kasa ta amince da shi a ranar 3 ga watan Disamba na shekarar 2025.

Taron ya sami halartar Ministan Kasafin Kudi da tsare-tsare na kasa Sanata Abubakar Atiku Bagugu da Karamar Minjstar Kudi Dorris Uzoka Anite da Ministan Albarkatun man fetir Sanata Heiniken Lokpobiri da Babban Akanta Janar na tarayya Babatunde Ogunjimi da kuma shugaban Hukumar Tattara kudaden shiga ta tarayya Zacch Adedeji.

A cewar Ministan Kudi Wale Edun kaso 30 cikin dari kacal na kasafin kudin shekarar 2025 aka iya aiwatarwa a inda kaso 70 a cikin dari za a haura da su zuwa sabuwar shekarar 2026.

You may also like

Leave a Comment