Home NewsHon. Shaaban Ibrahim Sharada OON, na taya tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano Hon. Kabiru Alhassan Rurum, murnar cika shekaru 56 a duniya.

Hon. Shaaban Ibrahim Sharada OON, na taya tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano Hon. Kabiru Alhassan Rurum, murnar cika shekaru 56 a duniya.

Hon. Shaaban Ibrahim Sharada OON, tsohon ɗan takarar gwamnan Kano, na taya tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, kuma dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure a majalisar tarayya Hon. Kabiru Alhassan Rurum, murnar cika shekaru 56 a duniya.

Yana mai bayyana shi a matsayin shugaba nagari mai kishin ƙasa da jajircewa wajen hidimtawa al’umma.

Sharada ya ce Rurum mutum ne da ya sadaukar da kansa wajen samar da zaman lafiya da ci gaban al’umma, musamman ta fuskar haɗin kan ’yan siyasa da inganta fahimtar juna.

Ya bayyana cewa irin rawar da Rurum ke takawa wajen jagoranci da kyakkyawan halayen da yake nunawa su ne manyan darussa ga matasa masu neman zama shugabanni a nan gaba.

You may also like

Leave a Comment