Home NewsAmurka za ta ‘shiga dumu-dumu’ cikin harkokin man Venezuela – Trump

Amurka za ta ‘shiga dumu-dumu’ cikin harkokin man Venezuela – Trump

Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce ya faɗa wa shugaban Venezuela cewa ya miƙa wuya mako guda kafin harin da Amurka ta kai yau tare da kama shi.

Yayin zantawarsa da kafar yaɗa labarai ta Fox News, Shugaba Trump ya ce daga yanzu Amurka za ta ”shiga dumu-dumu” cikin harkokin man Venezuela.

Ya ƙara da cewa mako guda da ya wuce ya yi magana da Maduro, inda ya shaida masa cewa ”ya kamata ka haƙura ka mika wuya”.

You may also like

Leave a Comment