Yaki Ya Dauki Zafi: Rasha Ta Harba Makami Mai Karfin Nukiliya Ukraine
Rasha ta yi amfani da makamin Oreshnik, wani makami mai linzami na zamani da ke tashi da gudu mai tsananin gaske, a hare-haren da ta kai kan wasu wurare a Ukraine Masana sun bayyana cewa Oreshnik na da karfin zuwa wurare da dama, abin da ke kara tsananta barazanar da yake haifarwa a wajen da aka harba shi Harin ya kara tayar da hankalin kasashen duniya, musamman ganin cewa an kai shi ne a yankin yammacin Ukraine da ke makwabtaka da kasashen da ke karkashin NATO
Russia – Sabon mataki da Rasha ta dauka na amfani da makamin Oreshnik a yakin Ukraine ya sake jawo hankalin duniya kan irin makaman zamani da ake amfani da su a rikicin da ya shafe shekaru uku yana gudana
Russia – Sabon mataki da Rasha ta dauka na amfani da makamin Oreshnik a yakin Ukraine ya sake jawo hankalin duniya kan irin makaman zamani da ake amfani da su a rikicin da ya shafe shekaru uku yana gudana.
Vladimir Putin yana wani bayani ga ‘yan jarida. Hoto: Getty Images Source: Getty Images New York Times ta wallafa cewa Rasha ta taba harba wannan makami a watan Nuwamban 2024, inda aka ce an yi amfani da shi domin gwaji. Bayani kan makamin da Rasha ta harba Oreshnik makami ne mai linzami da ke iya kai hari daga nesa, kuma yana tafiya da gudu fiye da na yawancin makaman da ake da su a yanzu. An gina shi ne bisa tsarin RS-26 Rubezh, wanda tun da farko aka kirkiro shi a matsayin makami mai kai hari daga nahiyoyi zuwa nahiyoyi. Daya daga cikin manyan siffofinsa shi ne tafiya mai nisa da daukar manyan makaman da za su iya kai hari wurare daban-daban a lokaci guda. Wannan fasali yawanci ana danganta shi ne da manyan makaman ICBM, abin da ya sa Oreshnik ya zama na daban a makaman Rasha. Makamin Oreshnik na da karfin nukiliya Shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya taba bayyana cewa ba za a iya dakile makamin Oreshnik ba, kuma karfinsa na iya kaiwa kusan na makamin nukiliya