Jam’iyyar NNPP ta ƙasa ta bayyana cewa dambarwar siyasar da ake yi a Jihar Kano ba za ta taba sa jam’iyyar ta rushe ba,

Jam’iyyar NNPP ta ƙasa ta bayyana cewa dambarwar siyasar da ake yi a Jihar Kano ba za ta taba sa jam’iyyar ta rushe ba, koda kuwa raɗe-raɗen da ake yi na cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf zai sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC ya tabbata.
Jam’iyyar ta nuna kwarin gwiwar cewa tana da tsarin da zai sa ta ci gaba da wanzuwa a matsayin gagarumar runduna.
​Fitacciya ta rawaito cewa, kakakin jam’iyyar NNPP na ƙasa, Ladipo Johnson, shi ne ya bayyana haka a matsayin martani ga yanayin siyasar Jihar Kano da ake ciki a halin yanzu. Johnson ya jaddada cewa kodayake jam’iyyar tana fatan dinke duk wata baraka da ke tsakanin shugabanninta, amma rashin mutum ɗaya ba zai sa tafiyar ta tsaya ba.
​Kamar yadda jaridar Punch ta wallafa, Johnson ya bayyana cewa jam’iyyar NNPP ba ta wani mutum ɗaya ba ce, illa dai jam’iyya ce ta jama’a dake da manufa ta gari ga ƙasar nan. Ya ƙara da cewa jam’iyyar tana sane da duk wani yunƙuri na rarraba kan mambobinta, amma sun shirya tsaf domin fuskantar ƙalubalen siyasar da ke tunkarar su.
​Rahoton na Punch ya kuma nuna cewa, kakakin ya buƙaci magoya bayan jam’iyyar da su kwantar da hankulansu, inda ya bayyana cewa jam’iyyar tana da kyakkyawar alaƙa da jama’ar gari, kuma hakan ne ya sa suka samu nasara a baya, kuma hakan ne zai sake ba su nasara a nan gaba.
Wannan sanarwa dai tana zuwa ne a daidai lokacin da tattaunawa ta yi zafi kan makomar siyasar Gwamna Abba Yusuf da kuma jagoran jam’iyyar, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

You may also like

Leave a Comment