Home NewsGwamnatin Yemen ta ce an kwato yankunan kudancin kasar daga hannun ‘yan awaren STC

Gwamnatin Yemen ta ce an kwato yankunan kudancin kasar daga hannun ‘yan awaren STC

Gwamnatin Yemen ta ce an kwato yankunan kudancin kasar daga hannun ‘yan awaren STC

 

Gwamnatin Yemen da kasashen duniya suka amince da ita ta bayyana cewa ta kwato yankunan kudancin kasar daga hannun ‘yan awaren kudancin kasar STC, wadda yanzu haka ke cikin ruɗani bayan da aka samu rarrabuwar kawuna a cikin ƙasar da kuma gudun hijira da shugabanta yayi.

 

Dakarun sojin Yemen a yankin kudancin ƙasar

Dakarun sojin Yemen a yankin kudancin ƙasar

 

Rashad al-Alimi, shugaban majalisar jagorancin kasa da Saudiyya ke marawa baya, a wata sanarwa da aka fitar a gidan talabijin na ƙasar a jiya Asabar, ya ce an mayar da dukkan garuruwan da ake gwabza faɗa karkashin ikon dakarun gwamnati.

 

Alimi ya ƙara da cewa matsayisa na shugaban kasar kuma babban kwamandan sojojinta, yana tabbatar wa da al’umarsa cewa an kwato Hadramout da al-Mahra, yanzu haka ba sa ƙarƙashin ikon ƴan aware.

 

Sannan wani rahoton da aka samu daga Riyadh babban birnin kasar Saudiyya, ya bayyana cewa ansamu tabbaci daga gwamnatin Yemen cewa a yanzu dakarunta sun ƙarɓe ikon dukkanin sansanonin soji da ke ƙarƙashin ikon ƴan aware na ƙasar a cikin ‘yan makonnin nan

You may also like

Leave a Comment