Home NewsMe ya sa Alonso ya raba gari da Real Madrid?

Me ya sa Alonso ya raba gari da Real Madrid?

An ga wasu bidiyoyi da suka yaɗu, inda Kyian Mbappe ke yi wa abokan wasansa wata alamar da ke nuna yana son su bar fili bayan kammala wasan da ƙungiyar ta yi rashin nasara a wasan ƙarshe na kofin Spanish Super Cup da aka buga a Saudiyya.

A cikin bidiyon an ga yadda Xabi Alonso ya buƙaci Mbappe ya tsaya, amma sai ɗan wasan ya dage, sai kuma aka ga daga ƙarshe Alonso ya haƙura, inda ya bi muradin Mbappe suka fice daga filin.

Lamarin da ya hana ƴan wasan yi wa tawagar Barcelona tsayuwar girmamawa domin karɓar kofin bayan lashe shi a karshen mako.

Masana ƙwallon ƙafa da dama suna kallon hakan a matsayin rashin girmama wasanni, wani abu da ba a taɓa alaƙanta wa da Alonsa ba.

Haka kuma hakan ya nuna cewa ba ƴan wasan ne ke juya ƙungiyar ba kocin ba.

Bayan hakan ne kuma Xabi ya sauya tunani game da aikinsa.

Amma wannan ba ritaya ba ce, ba abu ne kuma da ya shiryawa ba.

Ba a yi tsammanin Alonso zai bar Madrid ba – wata bakwai da rabi bayan fara horas da ƙungiyar da ya taka wa leda a baya.

You may also like

Leave a Comment