Iran ta zargi Trump da tayar da rikicin zanga-zanga a ƙasar

 

Iran ta zargi Shugaban Amurka, Donald Trump, da tayar da hankali ta hanyar zanga-zangar da ke gudana a kasar, inda ta ce barazanar da ya yi ta sa lamarin ya rikide zuwa tashin hankali.

 

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya ce zanga-zangar ta kara muni ne bayan Trump ya yi barazanar daukar matakin soja, yana mai ikirarin cewa ‘yan ta’adda sun shiga lamarin domin jawo tsoma bakin kasashen waje.

 

Araghchi ya ce hukumomin Iran sun samu nasarar shawo kan lamarin, kuma suna da bidiyoyin da ke nuna ana rarraba makamai ga masu zanga-zanga.

 

Ya kuma gargadi Amurka da kada ta tsoma baki, yana mai cewa Iran a shirye take ta kare kanta.

 

Zanga-zangar ta fara ne sakamakon matsanancin matsin tattalin arziki, kuma ta bazu zuwa sassan kasar da dama.

 

A cewar HRANA, sama da mutane 500 sun mutu, yayin da dubban mutane suka shiga hannun hukuma.

 

Trump ya ce Amurka na shirye ta tsoma baki idan aka kashe masu zanga-zangar, amma Iran ta ce duk wani hari zai haifar da martani mai tsauri.

You may also like

Leave a Comment