Home NewsTrump ya umarci Venezuela ta katse duk wata hulɗa da ƙasashen China da Rasha nan take.

Trump ya umarci Venezuela ta katse duk wata hulɗa da ƙasashen China da Rasha nan take.

Trump ya umarci Venezuela ta katse duk wata hulɗa da ƙasashen China da Rasha nan take.

 

Masana harakokin da suka shafi yaƙi, sun bayyana cewar Amurka na son yin yaƙi da ƙasashen Rasha, China, da Iran, don ta gwada ƙarfin makamanta a kansu, kuma a shirye take da tayi hakan, saboda ta gama tsara yadda yaƙin zai kasance, kuma ba zai shafi tattalin arziƙinta ba kasancewar ta samu nasarar karɓe iko da ƙasar Venezuela wacce tafi ko wace ƙasa yawan albarkatun man fetur a faɗin Duniya.

 

Masanan sun ce tun zangon mulkin shugaba Trump na farko yaso gwabza yaƙi da manyan ƙasashen na Duniya to amma a wancen lokaci ya san cewa ba zai samu goyon bayan Amurkawa ba, saboda basu son a ɓarnata arziƙinsu a fagen daga.

 

Amma a halin yanzu Amurka ta samu nasarar mamaye Venezuela, wacce da kuɗin man fetur ɗinta za ayi amfani wajen gudanar da yaƙin yayin da su kuma sauran ƙasashen irin su Rasha, China, Iran, basu da wata makama dole sai dai suyi amfani da dukiyar ƙasashen su.

You may also like

Leave a Comment