Home NewsƳanbindiga 80 sun miƙa wuya ƙarƙashin shirin afuwa na jihar Cross Rivers

Ƴanbindiga 80 sun miƙa wuya ƙarƙashin shirin afuwa na jihar Cross Rivers

Rundunar sojin Najeriya ta samu gagarumar nasara a yaƙin da suke yi a ayyukan ƴanbindiga bayan da wasu gomman masu ɗauke da makamai suka miƙa wuya bisa raɗin kai ƙarƙashin shirin afuwa da gwamnatin jihar Cross Rivers ta ɓullo da shi.

Cikin wata sanarwa da rundunar sojin ta wallafa a shafinta na X a ranar Juma’a ta ce aƙalla ƴanbindiga 80 da ke ayyukan satar mai a cikin teku suka miƙa kansu tare da ajiye makaman karƙashin shirin afuwar gwamnatin jihar da ke kudu maso kudancin ƙasar.

ƴanbindigaAsalin hoton,Nigerian Army/X
Rahotonni sun ce yanbindigar sun isa wurin shirin afuwar daga sansanoni biyu, na farko ƙarƙashin jagorancin ThankGod Ebikontei, da aka fi sani da Ayibanuagha, wanda ya gabatar da mayaƙa 39.

Sai kuma dabar John Isaac, da aka fi sani da Akpokolo mai jagorantar dabar da ake yi wa laƙabi da Border Boys, wanda ya gabatar da mayaƙa 41.

You may also like

Leave a Comment