Home Newscocin C and S da ke Kurmin Wali a Kaduna inda aka sace mutane

cocin C and S da ke Kurmin Wali a Kaduna inda aka sace mutane

Ga wasu hotuna da ke nuna cocin Cherubim and Seraphim da ke Kurmin Wali, wani a ƙauye a Kaduna da ke fama da matsalar tsaro inda aka sace mutane a lokacin da suke ibada.

An sace mutum 92 daga wannan cocin yayin da masu bauta ke gudanar da taron addini.

Wannan lamari ya zama wani abin damuwa cikin jerin sace-sacen da ke ci gaba da afkuwa a yankunan Arewa maso Yammacin Najeriya, wanda ya janyo fargaba ga jama’a.

Mutum 170 ne gaba ɗaya aka sace daga ƙauyen inda aka yi musu ƙofar raggo tare da kora su zuwa daji amma daga baya al’ummar sun bayyana cewa mutane 10 sun samu tserewa daga hannun ƴan bindigar.

A yau Talata ne al’ummar yankin suka fitar da sunayen waɗanda aka sace

You may also like

Leave a Comment