Gwamnatin jihar Legas ta bayar da umarnin gudanar da binciken musabbabin mutuwar wasu tagwaye, waɗanda aka bayar da rahoton mutuwarsu kwana guda bayan yi musu allurar riga-kafi a wata cibiyar allurar da ke jihar.
Lamarin ya ɗauki hankali ne bayan da mahaifin yaran mai suna Samuel Alozie – da aka fi sani da Promise Samuel a dandalin TikTok – ya wallafa bidiyon gawarwakin tagwayen yayin da yake bayyana yadda suka mutu bayan yi musu riga -kafin.
Daga baya kuma ya sake wallafa wani bidiyo inda yake cewa a ranar 24 ga watan Disamban da ya gabata sun kai tagwayen riga-kafi ne kamar yadda suka saba kai su a baya, sai dai ya ce a wannan karon yaran sun jigata bayan yi musu riga-kafin.
“Ba sa iya cin abinci, ba sa yin wasa, ba ma sa rigimar da suka saba yi a baya, sun kasance cikin kasala,” in ji shi.
Ya ci gaba da cewa ma’aikatan lafiyar da suka yi riga-kafin sun ce a ba su maganin zazzaɓi idan jikinsu ya yi ɗumi, abin da kuma ya ce sun yi shi mahaifiyarsu, har ma wanka suka yi musu da ruwan sanyi domin jikin nasu na sauka daga zafin zazzaɓin amma hakan ba ta samu ba.
Inda ya ce daga ƙarshe duka yaran biyu suka mutu bayan kwana guda da yi musu zazzaɓin.
Lamarin ya sake tasowa ne bayan mutuwar ɗaya daga cikin tagawayen fitacciyar marubuciyar nan Chimamanda Adichie, wadda ta zargi asibiti da sakacin mutuwar ɗan nata.
Zargin jami’an lafiya da sakaci wajen mutuwar marasa lafiya ya jima yana karakaina tsakanin wasu ƴan ƙasar.
Ko a makon da ya gabata ma hukumomi a jihar Kano sun dakatar da wasu likitoci bayan da suka manta alkamashin tiyata a cikin wata mata, lamarin da ya kai ga mutuwarta.