Gwamnatin tarayya ta amince da raba fiye da Naira biliyan 32 ga jihohi 36 na tarayya da Babban Birnin Tarayya (FCT) domin ƙarfafa ayyukan kula da lafiya na matakin farko da kuma faɗaɗa ɗaukar inshorar lafiya.
Matakin amincewar ya faru ne ayayin ayain taron kwamitin sa idi na ministoci na shekarar 2025 wanda Ma’aikatar Lafiya da Jin Ƙai ta Tarayya ta gudanar a ranar Juma’a a Abuja.
A cewar Babbar Sakatariyar Ma’aikatar lafiya ta tarayya Kachallom Daju, za a saki kashi na hudu na kudaden ga jahohin Nigeria a karkashin shirin Asusun tallafawa Kiwon lafiya kamar yadda kudirin gwamnatin tarayya ya tanada a fannin kiwon lafiya.
Ta ce ana sa ran kuɗaɗen za su taimaka wajen inganta ayyuka a cibiyoyin kula da lafiya na matakin farko, tare da ƙara adadin masu shiga inshorar lafiya, da kuma ƙarfafa muhimman matakan kula da kiwon lafiya a Nigeria.