Home NewsHukumar Bunƙasa Asusun Ci Gaban Aikin Noma ta Ƙasa ta ƙaddamar da kashi na farko na Shirin Tallafa wa Manoman Albasa, a jihar Sokoto, wanda manoman albasa 600 za su amfana.

Hukumar Bunƙasa Asusun Ci Gaban Aikin Noma ta Ƙasa ta ƙaddamar da kashi na farko na Shirin Tallafa wa Manoman Albasa, a jihar Sokoto, wanda manoman albasa 600 za su amfana.

Hukumar Bunƙasa Asusun Ci Gaban Aikin Noma ta Ƙasa ta ƙaddamar da kashi na farko na Shirin Tallafa wa Manoman Albasa, a jihar Sokoto, wanda manoman albasa 600 za su amfana.

Babban Sakatare kuma Shugaban Hukumar NADF, Muhammad Abdul Ibrahim, ne ya ƙaddamar da shirin a hukumance, inda Mataimakin Babban Sakatare na hukumar, Mu’azu Ibrahim, ya wakilce shi.

Da yake jawabi a wajen taron, Ibrahim ya ce shirin an tsara shi ne domin taimaka wa manoma su farfaɗo daga asarar da ambaliyar ruwa da sauyin yanayi suka haifar, da dawo da ƙarfin samarwa, tare da ƙarfafa juriyar sashen noman albasa.

Ya bayyana cewa manoman albasa a jihohin Sokoto, Kebbi, Yobe da Borno na daga cikin waɗanda ambaliya ta fi shafa, yana mai jaddada cewa bala’o’in sun tarwatsa hanyoyin rayuwa, kasuwannin cikin gida da kuma wadatar abinci a ƙasa baki ɗaya.

A cewarsa, shirin wanda ake aiwatarwa tare da haɗin gwiwar gwamnatocin jihohi da sauran masu ruwa da tsaki ya fara ne da rabon muhimman kayan aikin gona, kuma ya yi daidai da shirin nan ma sabunta fatan yan Najeriya na shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Ya tabbatar wa waɗanda suka amfana cewa za a gudanar da aikin bisa gaskiya, riƙon amana da adalci, yana mai ƙara da cewa an tantance dukkan kayan tallafin yadda ya kamata domin su kai ga manoma na gaskiya.

You may also like

Leave a Comment