Home EntataimentKamfanin Dangote Refinery ya sake rage farashin Fetur daga N828 zuwa N699 a kowace lita, an samu ragin da ya kai N129 ko kusan kashi 15.6%.

Kamfanin Dangote Refinery ya sake rage farashin Fetur daga N828 zuwa N699 a kowace lita, an samu ragin da ya kai N129 ko kusan kashi 15.6%.

Shafin Petroleumprice.ng ya nuna sabbin bayanan farashin da suka fara aiki daga ranar 11 ga Disamba, 2025.

Wani jami’in kamfanin ya tabbatar da saukar farashin, wanda shi ne karo na 20 da kamfanin ke sake daidaita farashin fetur a bana.

Sabon ragin na zuwa ne kwanaki biyar bayan Aliko Dangote ya ce kamfanin zai ci gaba da sauke farashi domin zama abokin gogayya da kayayyakin da ake shigo da su daga waje.Dangote ya ce farashin zai ci gaba da raguwa yayin da masana’antar ke kara samarwa da kuma inganta gasa da man da ake shigo da shi.

You may also like

Leave a Comment