Home NewsShugaba Bola Ahmad Tinubu zai gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2026 a zaman haɗin gwiwa na Majalisar Tarayya a ranar Juma’a da misalin ƙarfe 2 na rana.

Shugaba Bola Ahmad Tinubu zai gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2026 a zaman haɗin gwiwa na Majalisar Tarayya a ranar Juma’a da misalin ƙarfe 2 na rana.

Za a tsaurara tsaro a harabar majalisar, kuma duk waɗanda ke da aiki a majalisar dole ne su kasance a waje aiki kafin ƙarfe 11 na safe.
Hakazalika, Tinubu ya nemi Majalisar ta soke tare da sake tabbatar da kasafin kuɗin 2026 wanda ya kai Naira tiriliyan 43.56.
Manufar wannan mataki ita ce kada a yi aiki da kasafin kuɗi da yawa a lokaci guda, sannan a tabbatar da bin diddigin kashe kuɗi, musamman a ayyuka masu buƙatar kulawar gaggawa da tsaron ƙasa.

An tsara wannan shiri ne don ƙarfafa tsari wajen kashe kuɗi da tabbatar da cewa kuɗaɗen ana amfani da su kamar yadda Majalisar ta amince.

Masana sun yi gargaɗin cewa tsawaita kasafin kuɗi na iya haifar da
ruɗani, maimaitawa, da rashin tsara ayyuka yadda ya kamata, wanda zai iya shafar ci gaban tattalin arziƙi da kuma amincewar masu zuba jari.

Masana sun ƙara da cewa yawaitar ciyo bashin gwamnati yana rage damar kashe wa sabbin ayyuka kuɗi. Ingantaccen tsarin biyan bashi, in ji su, yana da muhimmanci wajen samun ƙarin kuɗi don ci gaba da tabbatar da cewa manufofin kasafin kuɗi sun cika.

Kwamitin Kasafin Kuɗi na Majalisar Tarayya zai duba kuɗaɗen da aka gabatar kafin a amince da su gaba daya, kuma gwamnati na fatan wannan mataki zai samar da tsarin kashe kuɗi na gaskiya da kuma bin doka.

You may also like

Leave a Comment