Home NewsƘungiyar Ɗalibai ta Najeriya ta sanar da fara zanga-zanga kan sabuwar dokar haraji

Ƙungiyar Ɗalibai ta Najeriya ta sanar da fara zanga-zanga kan sabuwar dokar haraji

Ƙungiyar Ɗalibai ta Najeriya, NANS ta fara shirin wayar da kan ɗalibai domin gudanar da zangaz-zanga a faɗin ƙasar domin nuna rashin amince wa da aiwatar da sabuwar dokar haraji da ta fara aiki a ranar 1 ga watan nan na Janairun 2026.

Shugaban ƙungiyar, Olushola Oladoja ya ayyana ranar 14 ga watan Janairun 2026 a matsayin ranar ɗaukar mataki kan dokar a Najeriya .

A wata sanarwa Oladoja ya nuna rashin dacewar aiwatar da dokar a ranar 1 ga watan na Janairu a daidai lokacin da kiraye-kiraye suka yawaita kan a dakatar da ita saboda zargin cushe.

Ya ƙara da cewa ƙaddamar da dokar harajin “ba wai kawai abin takaici ba ne wani abu ne mai haɗari ga gwamnatin da take ikrarin aiwatar da tsare-tsare na jama’a da kuma bin ƙa’idodjin dimokraɗiyya.”

You may also like

Leave a Comment