Sabon faɗa ya ɓarke tsakanin sojoji da ƴan tawayen MPRD a C
A Chadi, sabon faɗa ya ɓarke tsakanin dakarun gwamnati da ƴan tawayen MPRD, lamarin da ya yi sanadin rayukan gwamman mutane daga dukkan ɓangarorin biyu.
Sabon faɗan ya ɓarke ne bayan gwamnatin Chadi ta aike da dakarunta zuwa yankin Moyen-Chari da ke kusa da iyakar Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya
Babban sakataren ƙungiyar ƴan tawayen MPRD Luc Beyam ya ce dakarun gwamnatin sun yi yunƙurin yiwa jami’ansu ƙawanya, kodayake wata majiya daga mahukuntar ƙasar na cewa ƴan tawayen sun tsara kai musu harin kwantom ɓauna ne.
Tsawon jiya Talata aka shafe ana gwabza rikicin tsakanin ɓangarorin biyu, da ƴan tawayen ke iƙirarin cewa sun fi yiwa sojojin illa, yayin da gwamnati ba ta ce komai ba kawo yanzu.
Wannan musayar wuta na zuwa ne bayan shafe watanni ana tattaunawa tsakanin hukumomin ƙasar da ƴan tawayen don cimma yarjejeniyar zaman lafiya, da N’Djamena ke neman su ajjiye makamansu.
To sai dai ƙungiyar MPRD ta ce gwamnatin Chadi ta gaza biya musu buƙatunsu, hakan ne yasa ta ke matsa musu lamba su ajjiye makamai ba bisa raɗin kan