Home NewsHarin ƴan aware a yankin Anglophone na Kamaru ya kashe mutane 14

Harin ƴan aware a yankin Anglophone na Kamaru ya kashe mutane 14

Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama da masu fafutukar kare al’umma sun yi allawadai da harin da ake zargin ƴan awaren Anglophone ne suka kai a ƙauyen Fulani a arewa maso yammacin Kamaru, wanda ya kashe mutane 14 a ranar Laraba.

Gwamnan yankin, Adolphe Lele Lafrique ya ce maharan sun buɗe wuta yayin da yawancin mazauna yankin ke barci tare da ƙona gidaje da kashe dabbobi sannan sun kuma sace babura.

Mutum 10 kuma sun jikkata a harin ciki har da yara biyu, waɗanda ake kula da su a asibiti.

Lauyan kare hakkin ɗanadam, Felix Agbor Balla ya ce kai wa fararen hula hari laifi ne mai tsanani a ƙarƙashin dokar ƙasashen duniya, yana mai kira a gudanar da bincike mai gaskiya da adalci don gano masu laifin.

Tun daga shekarar 2017 ne rikici tsakanin ƴan aware da gwamnati a yankunan Anglophone biyu na Kamaru ya kashe kimanin mutum 6,000 tare da tilastawa sama da rabin miliyan barin gidajensu.

You may also like

Leave a Comment