A jihar Borno, Shugaba Tinubu zai ƙaddamar da wasu manyan ayyuka na raya ƙasa da gwamnatin jihar tare da haɗin gwiwar gwamnatin tarayya suka aiwatar, tare da ganawa da manyan jami’an tsaro da shugabannin al’umma domin duba halin tsaro da walwalar jama’a.
A Bauchi, shugaban zai kai ziyara ta ta’aziyya ga gwamnatin jihar da iyalan fitaccen malamin addini, marigayi Sheikh Dahiru Bauchi, inda ake sa ran zai jajanta musu tare da jaddada muhimmancin zaman lafiya da haɗin kai a ƙasar nan.
Bayan haka, Shugaba Tinubu zai wuce Lagos, inda zai ci gaba da wasu muhimman aiki, tare da shirin yin hutun ƙarshen shekara.
Ziyarar na nuni da kudirin shugaban ƙasa na kusantar al’umma,da sa ido kan ayyukan raya ƙasa, da kuma ƙarfafa
zaman lafiya da tsaro a sassa daban-daban na Najeriya.