Home NewsYan tawayen masu tada ƙayar baya na M23 a kasar Rwanda sun bayyana shirinsu na ficewa daga garin Uvira na yankin gabashin Congo bayan buƙatar yin hakan da Gwamnatin ƙasar Amurka ta gabatar mata.

Yan tawayen masu tada ƙayar baya na M23 a kasar Rwanda sun bayyana shirinsu na ficewa daga garin Uvira na yankin gabashin Congo bayan buƙatar yin hakan da Gwamnatin ƙasar Amurka ta gabatar mata.

Yan tawayen masu tada ƙayar baya na M23 a kasar Rwanda sun bayyana shirinsu na ficewa daga garin Uvira na yankin gabashin Congo bayan buƙatar yin hakan da Gwamnatin ƙasar Amurka ta gabatar mata.

Gwamnatin kasar Amurka dai ta yi suka ne kan kame garin da Yan tawayen suka yi a makon da ya gabata da kuma bayyana shi a matsayin tarnaƙi ga shirin shiga tsakanin bangarorin da basa ga maciji da juna.
Ƴan tawayen M23 dai sun shiga garin Uvira da ke a kan iyakar ƙasar Rwanda da Burundi ne kasa da mako daya bayan haɗuwar shugabannin kasashen Congo da Rwanda da shugaban Amurka Donald Trump a birnin Washington DC, haɗuwar da ta ba da tabbacin shirinsu na tattaunawar samar da zaman lafiya  .

A ranar Asabar da ta gabata ne Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya zargi Rwanda da ƙoƙarin lalata tattaunawar samar da zaman lafiya da a ka yi a birnin Washington DC tare da shan alwashin ɗaukar matakin tabbatar da ganin an mutunta alƙawurran da su ka yi wa shugaban kasar ta Amurka na samar da zaman lafiya.

To sai dai ƙasar Rwanda ta musanta zargin taimaka wa ƴan tawayen M23, amma kuma ta zargi jami’an sojin Congo da Burundi kan zafafa tarzomar.

Wani Rahoto da wata kungiya a karkashin kulawar Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a watan Yulin da ya gabata ya nuna yadda ƙasar Rwanda ke bada Umarnin ga yan tawayen a fakaice.

Amma Corneille Nangaa shugaban ɓangaren M23 masu alaƙa da ƴan tawayen Congo ya faɗa a shafinsa na X cewar yan tawayen za su janye daga yankin kwata kwata.

You may also like

Leave a Comment