167
Shugaban hukumar kula da albarkatun man Fetur NMDPRA Injiniya Farouk Ahmed ya yi murabus daga mukaminsa.
Hakan ya biyo bayan taƙaddama tsakaninsa da Alhaji Aliko Dangote, lamarin da ya kai Dangote ya shigar da korafi ga hukumar ICPC.
Tuni dai shugaba Tinubu ya amince da murabus din nasa tare da tura da sunan Injiniya Saidu Aliyu Mohammed ga majalisar dattawa domin tantance shi a matsayin sabon Shugaban hukumar ta NMDPRA.