Home NewsShugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa za a wadata ‘Yan sandan jahohi da za a kaddamar da makamai.

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa za a wadata ‘Yan sandan jahohi da za a kaddamar da makamai.

Tinubu ya bayyana hakanne a Babban Dakin taro da ke a fadar shugaban Kasa a Abuja.

Hakanan shugaban Kasa ya bayyana shirye- shiryen da ake na samar da Dakarun kare gandun daji wadanda su ma ya ce za a karafafe su da makamai, domin su murkushe ta’addanci da kuma ‘Yan bindiga a fadin Nigeria.

Hakanan ita ma Majalisar Dokoki ta kasa ta bayyana mara baya ga samar da ‘yan sandan Jahohi dukkuwa da yadda wasu su ke bayyana fargaba da yadda Gwamnonin jahohi za su iya shige gona da iri da su.

You may also like

Leave a Comment