115
Ministan ya bayyana hakanne ayayin kaddamar da fara gasar kwallon kwando ta kwanaki uku wadda aka shiryawa matasa.
Gasar ta Kwallon kwando wadda gidauniyar Bosun Tijjani ta shirya an gudanar da ita ne a cibiyar harkokin wasanni da ke Abeakuta a jahar Ogun.
A cewar ministan an tsara gasar ne domin samar da walwala ga matasa tare da kyautata Koshin lafiyarsu. Ministan ya ce manufar kowacce irin gasar motsa Jiki shi ne gina al’umma ba tare da la’akari da tushen su ba.
Hakanan Ministan ya ce gwamnatin tarayya ta Kudiri aniyar bullo da Kirkire-kirkire da za su ba da damar karfafa guiwar matasa domin habaka cigaban kasar nan.