147
Dakarun Rundunar Sojin Najeriya na Birged ta 6, ƙarƙashin Sashen 3 na Operation Whirl Stroke (OPWS), sun cafke wani shahararren shugaban ’yan bindiga da ake zargi da hannu a garkuwa da mutane da fashin makami a yankin Benue–Taraba.
A wata sanarwa da Birged ɗin ta fitar ranar Litinin, an bayyana cewa an kama wanda ake zargin ne a ranar 21 ga Disamba, 2025, ta hannun dakarun sansanin gaba na soji (FOB) Wukari, bayan samun sahihan bayanan sirri, a ƙauyen Vaase da ke ƙaramar hukumar Ukum a jihar Benue.
An bayyana sunan wanda aka kama da Fidelis Gayama, wanda jami’an tsaro ke kallon sa a matsayin babbar manufa (high value target), kuma ya daɗe yana cikin jerin mutanen da ake nema ruwa a jallo.
Binciken farko ya nuna cewa Gayama na da alaƙa ta kut-da-kut da Aka Dogo, wani shahararren jagoran ƙungiyar ’yan bindiga da jami’an tsaro ke nema.
Ana kuma zargin Gayama da jagorantar wata ƙungiya da ta addabi matafiya da mazauna yankunan kan iyaka tsakanin jihohin Benue da Taraba, musamman a hanyar Kente zuwa Wukari.
Wasu majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa ’yan sanda a ofishin Vaase sun amince da cewa Gayama na cikin mutanen da sashen ’yan sanda na Beji a ƙaramar hukumar Ukum ya ayyana a matsayin wanda ake nema.
A cewar mukaddashin kakakin Birged ta 6, Laftanar Umar Muhammad, ana tsare da wanda ake zargin a hannun sojoji, kuma za a miƙa shi ga hukumomin da suka dace domin ci gaba da bincike da gurfanar da shi gaban shari’a.
Kwamandan Birged ta 6 kuma kwamandan Sashen 3 na OPWS, Birgediya Janar Kingsley Chidiebere Uwa, ya yaba wa dakarun bisa ƙwarewa da tsantsar bin doka wajen aiwatar da aikin, yana mai bayyana kamen a matsayin babban koma-baya ga ƙungiyoyin ’yan ta’adda a yankin.
Ya kuma jaddada ƙudirin rundunar na ci gaba da kai hare-hare domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da roƙon jama’a su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai a kan lokaci.