105
Jami’an Amurka sun ce masu gadin bakin teku sun tasa wani jirgin ruwa na dakon mai a yankin gabar tekun Venezuela gaba.
Wannan shi ne karo na biyu a ƙarshen makon nan da jami’an na Amurka ke bin wani jirgin ruwa a wannan yanki na Karebiya domin su kama shi.
Venezuela dai ta zargi Amurka da fashi da kuma satar mutane.
A wannan makon Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce ya bayar da umarnin hana shigarwa ko fitar da man da aka sanya wa takunkumi Venezuela.
Amurka ta yi zargin cewa jiragen na ɗauke da man da aka sanya wa takunkkumi, wanda ta ce ana amfani da kuɗinsa wajen tafiyar da ta’addanci na miyagun kwayoyi, amma kuma ba ta bayar da shedar hakan ba.