Home NewsA wani sako da ya wallafa ta shafinsa na X, shugaba Macron ya taya al’ummar Venezuela murnar rabuwa da mulkin dan kama karya,

A wani sako da ya wallafa ta shafinsa na X, shugaba Macron ya taya al’ummar Venezuela murnar rabuwa da mulkin dan kama karya,

A wani sako da ya wallafa ta shafinsa na X, shugaba Macron ya taya al’ummar Venezuela murnar rabuwa da mulkin dan kama karya,

yana mai cewa dole su kasance cikin farin ciki bayan da suka rabu da mutumin da ya riƙe dukkan madafun iko a hannunsa tare da tauye musu da hakoki.

Tun da farko, ministan harakokin wajen Faransa Jean- Noel Barrot ne ya soki abin da ya danganta da shishigin Amurka a harakokin cikin gidan Venezuela ya na mai bada shawarar amfani da hanyar siyasa domin warware batun maimakon ɗaukar matakin da ya saɓa wa dokar ƙasa da ƙasa.

Sai dai matsayar Emmanuel Macron ta sha bamban da ta galibin ƴan siyasar ƙasar wadanda su kayi tir da Allah- wadai da harin Amurka ta kai kan ƙasar Venezuela.

Fadar shugaban kasar Faransa Elysee ta fitar da sanarwa cewa a jiya asabar shugaban ƙasar Emmanuel Macron ya tattaunawa ta waya tarho da takwarorinsa na Amurka da Argentina a yayin da a gefe guda ya aike da sakon rubutu ga takwaransa na Brazil Lula Da Silva kan halin da aka shiga a Venezuela.

You may also like

Leave a Comment