Home NewsSojoji sun ceto fasinjojin da aka yi yunƙurin sacewa kan hanyarsu zuwa Kamaru

Sojoji sun ceto fasinjojin da aka yi yunƙurin sacewa kan hanyarsu zuwa Kamaru

Rundunar Sojin Najeriya ta ce sojojinta na 13 Brigade sun samu nasarar ceto fasinjoji 18, ciki har da jarirai 2, daga wani jirgin ruwa da ‘yan fashin ruwa suka kama a ranar 11 ga Janairu, 2026.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a shafinta na X.

Rahotanni sun nuna cewa ƴan fashin ruwa wadanda suka yi amfani da ƙananan jiragen ruwa masu gudu sun kai wa jirgin wanda ke tafe daga Najeriya zuwa Kamaru hari a gaɓar tashar kamun kifi ta Kombo a kogunan Kamaru

Sojoji sun samu kiran gaggawa kan lamarin inda suka yi saurin ɗaukar mataki suka bi ‘yan fashin abin da ya haifar da musayar wuta wanda ya sa ɗaya daga cikin jiragen ƴan fashin ya kife.

Sakamakon haka, ‘yan fashin suka tsere zuwa cikin koguna suka bar fasinjojin inda daga bisani sojojin suka ceto su cikin ƙoshin lafiya.

You may also like

Leave a Comment