Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta fara wani shiri na tattara bayanai a faɗin ƙasar nan wanda ke gudana a jihohi 36 na tarayya, inda a halin yanzu Jihar Kano ke karɓar wata babbar tawaga domin aiwatar da aikin.
Ziyarar na daga cikin ƙoƙarin ƙarfafa tsarin ƙididdiga da tabbatar da samun sahihan bayanai domin tsare-tsare da ci gaban ƙasa.
Jagoran tawagar shi ne Babban Mai Ƙididdiga na Ƙasa kuma Babban Daraktan Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa, tare da manyan jami’ai da abokan hulɗa. Cikin tawagar har da Wakilin UNICEF, Mista Wayne A. Bacale, Babban Jami’in Tsare-tsare da Saka Ido, da kuma Dakta Onoriode Ezire, Babbar Kwararriyar Lafiya kuma Jagorar Aikin IMPACT da World Bank ke tallafawa.
A yayin ziyarar tasu a Jihar Kano, Darakta Janar na Hukumar Ƙididdiga ta Jihar Kano ne ya tarɓi tawagar, daga nan aka jagorance su domin kai ziyarar girmamawa ga Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, sannan suka gana da Gwamnan Jihar Kano. A tattaunawar tasu, an jaddada muhimmancin sahihan bayanai wajen tsara manufofi da inganta ayyukan hidima ga al’umma.
A jawabinsa, Babban Jami’in Ƙididdiga na Jihar Kano, Dr. Surajo Ibrahim, ya bayyana cewa samun ingantattun bayanai cikin lokaci na da matuƙar muhimmanci wajen tsare-tsare a fannoni kamar lafiya, ilimi, noma da bunƙasar tattalin arziƙi.
Ya ƙara da cewa sahihan bayanai su ne ginshiƙin yanke shawara mai tasiri, domin suna bai wa gwamnati da masu ruwa da tsaki damar fahimtar buƙatun al’umma tare da tsara shirye-shiryen da suka dace.
A wani ɓangare na sa ido kan aikin, tawagar ta kai ziyara Danbagina, ƙauyen Jigawar Alhaji Ado da ke Ƙaramar Hukumar Dawakin Kudu. Sun duba yadda aikin ke gudana a fili tare da tattaunawa da masu tattara bayanai domin tantance ci gaba da ingancin bayanan da ake tattarawa daga gidaje da al’umma.
Tawagar ta kuma yi kira ga al’umma da su ba da cikakken haɗin kai ga masu tattara bayanai domin tabbatar da samun sahihan bayanai da za su amfani jama’a baki ɗaya.
Da yake jawabi yayin ziyarar, Shugaban Ƙauyen Danbagina, Malam Sa’adu Bako, ya nuna jin daɗinsa kan wannan shiri tare da tabbatar da cikakken haɗin kan al’ummarsa. Ya ce wannan aiki zai taimaka wajen kawo ci gaba mai ma’ana ga yankin.
Ana sa ran wannan shirin tattara bayanai na ƙasa zai ƙara inganta tsare-tsare bisa hujjoji tare da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomin gwamnati da abokan hulɗa, ciki har da UNICEF da Bankin Duniya, domin samar da ci gaba mai ɗorewa a faɗin Najeri
78