Home NewsCibiyar yada labarai ta Abba Kabir Yusuf (AKY Media Center) ta bayyana damuwa kan wasu tsoffin kwamishinoni da mambobin Kwamitin Zartarwa na Jihar Kano da suka ajiye mukamansu kwanan nan.

Cibiyar yada labarai ta Abba Kabir Yusuf (AKY Media Center) ta bayyana damuwa kan wasu tsoffin kwamishinoni da mambobin Kwamitin Zartarwa na Jihar Kano da suka ajiye mukamansu kwanan nan.

Sanarwar ta ce waɗannan jami’an sun ajiye mukamansu ne da kansu, suna nuna rashin goyon baya ga matakin gwamna na shiga jam’iyyar APC, sannan suna biyayya ga bangaren NNPP karkashin Rabiu Musa Kwankwaso.

Tun bayan ajiye mukamai, wasu tsoffin jami’an sun ki mayar da motoci na gwamnati da aka basu lokacin aiki. AKY Media Center ta jaddada cewa motoci ba kyauta bane, suna daga kadarorin gwamnati ne da aka bayar don aiki kawai, kuma dokoki sun umurci duk wanda ya kammala aiki da ya mayar da duk kayan gwamnati.

Sanarwar ta ce wasu sun riƙe fiye da mota guda, wasu kuma har motoci na Hilux da ake amfani da su wajen ayyukan gwamnati sun tafi da su. Duk kokarin hukumomi na tuntuba da umarni na mayar da motoci an yi watsi da su, abin da ke nuna rashin biyayya da rashin mutunta amana ta jama’a.

Cibiyar ta ce gwamnatin jihar ba za ta tsaya kallon wannan barnar ba, za a ɗauki duk matakan shari’a da na gudanarwa don dawo da motocin da kuma tabbatar da cikakken hisabi.

A ƙarshe, AKY Media Center ta yi kira ga tsoffin kwamishinonin da sauran mambobin Kwamitin Zartarwa su girmama wannan umarni su mayar da dukkan kadarorin gwamnati ba tare da bata lokaci ba, domin kare mutuncin su da kayan gwamnati ga al’ummar Jihar Kano.

You may also like

Leave a Comment