Home NewsIran ta gargaɗi Amurka kan taimaka wa masu zanga-zanga a ƙasar

Iran ta gargaɗi Amurka kan taimaka wa masu zanga-zanga a ƙasar

Iran ta gargaɗi Amurka kan taimaka wa masu zanga-zanga a ƙasar

 

Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta yi Allah-wadai da kuma bayyana goyon bayan da manyan jami’an Amurka ke nunawa ga zanga-zangar da ke faruwa a ƙasarta a kwanakin baya a matsayin “tsoma baki da kuma yaudara.”

 

A cikin wata sanarwa da gwamnatin Iran ta fitar, ta ce: “Matakan da Amurka ke ɗauka ba wai saboda tausayi ga mutanen Iran bane,sai dai domin sanya matsi da yin baraza da kuma katsalanda a al’amarun cikin gida na Iran domin tayar da tarzoma da tashin hankali, da haifar da rashin tsaro a ƙasar.”

 

Iran ta kara da cewa, “Abin da gwamnatin Amurka ke yi a yau ba kawai yaƙin tattalin arziki bane, har ma da yaƙi na tunani da yaɗa labaran ƙarya da barazanar shiga kai tsaye na soja, da kuma ƙarfafa tashin hankali.”

 

A cikin kwanaki 12 da suka gabata, manyan jami’an Amurka, ciki har da Shugaba Donald Trump, sun yi kira ga gwamnatin Iran da ta daina “kashe” masu zanga-zanga.

 

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta ce zanga-zangar na nuna “fushin mutanen Iran” kan rashin iya samar masu rayuwa mafi kyau.”

You may also like

Leave a Comment