Mahukuntan Libya sun gano wani makeken kabari ɗauke da gawarwakin ƴan ci rani
An gano gawarwakin ƴan ci rani aƙalla 21 a cikin wani makeken kabari a gabashin Libya, yayin da wasu ƙarin 10 dukkaninsu ƴan kudu da saharar Afrika suka tsira da ransu.
16/01/2026 – 15:50
Majiyoyin tsaro biyu ne suka tabbatar da tono gawarwakin ƴan ci ranin ƴan kudu da saharar Afrika a cikin makeken kabarin a yankin gabashin Libya.
Majiyoyin da suka nemi a sakaya sunansu sun ce, an gano ƴan ci ranin ne bayan wani samame da jami’an tsaron ƙasar suka kai wata gona dake kusa da garin Ajdabiya, bayan samun rahotannin cewa ana tsare dasu a yankin.
Jami’an tsaron sun ƙubutar da wasu ƴan ci ranin da aka tsare a yankin, waɗanda suka haɗa da mata da maza da kuma ƙananan yara, kodayake dukkansu suna cikin mawuyacin hali, kuma tuni aka garzawa dasu asibiti, yayin da aka kame mamallakin gonar da aka gano makeken kabarin.
Kawo yanzu babu wani ƙarin bayani dangane da yadda akai ƴan ci ranin suka rasa rayukansu, amma tuni aka ƙaddamar da bincike akai.
Wannan dai ba shi ne karon farko da ake gano irin waɗannan maka-makan kaɓurbura a Libya ba, baya ga gano tarin ƴan ci ranin da ƙungiyoyi ta’addanci ke garkuwa dasu tare da neman kuɗin fansa