92
Sojojin sun kuma kama wasu da ake zargin suna taimakawa ‘yan ta’adda.
Sanarwar ta ce, runduna ta 25 ce ta ta gano shirin yan ta’addar din ne yayin sintiri akan hanyar Damboa zuwa Komala.
Rahotanni sun shaida cewa an lalata bom din cikin aminci, abin da ya kauce wa yiwuwar hadari ga sojoji da fararen hula.
A wani aiki daban, sojojin a hanyar Maiduguri Zika Bama sun kama wata mota da ake zargin tana dauke da kayan tallafi da za a mika wa ‘yan Boko Haram da ISWAP.
An gano kayayyaki irin su abinci, da kayan sha,da wayoyin hannu da kuɗi, sannan an kama mutane biyu da ke cikin motar domin karin bincike.