’Yan Majalisar Dokokin Jihar Gombe guda biyu daga jam’iyyar PDP; Gabriel Galadima Fushison da ke wakiltar mazaɓar Kaltungo ta Yamma da Malon Nimrod Yari mai wakiltar mazaɓar Shongom, sun sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC.
An kai su fadar gwamnatin jihar, inda gwamna Inuwa Yahaya ya tarbe su tare da Shugaban Majalisar Dokokin Jihar, Abubakar Mohammed Luggerewo, mataimakinsa Sadam Bello.
’Yan majalisar sun ce sun sauya sheƙar ne saboda ayyukan ci gaba da gwamnan yake yi a faɗin jihar.
Duk da kasancewarsu a PDP, sun ce ba a nuna musu wariya ba, kuma mazaɓunsu sun amfana daga ayyukan gwamnati.
Ya ƙara da cewa APC na ci gaba da zama dandalin haɗin kai da shugabanci na gari.
Yanzu APC na da kujeru 23 daga cikin 24 na Majalisar Dokokin Jihar Gombe, wanda hakan ya ƙara nuna rinjayen jam’iyyar a siyasar jihar.