Majalisar Dattawa ta kasar nan ta fara muhawara
kan lissafin kasafin kuɗin shekarar 2026 da Shugaba
Bola Tinubu ya gabatar mata.
Shugaban masu rinjaye na majalisar, Sanata
Opeyemi Bamidele, ya jagoranci tattaunawar kan
wannan gagarumar shawara ta kashe kuɗi har Naira
tiriliyan 58.47 a 2026.
Yayin gabatar da ƙa'idodin lissafin, Bamidele ya
bayyana wa majalisar cewa wannan doka ita ce
matakin shari'a na aiwatar da kasafin kuɗin 2026, a
cewar rahoton Punch.
Ya bayyana kasafin a matsayin ginshiƙin gudanar da
gwamnati da tattalin arziki, yana mai jaddada cewa
shi ne yake mayar da manufofin shugaban ƙasa zuwa
ayyukan gwamnati na zahiri.
Game da yanayin tattalin arziki kuwa, shugaban
masu rinjayen ya ce an tsara kasafin kudin 2026 ne a
daidai lokacin da ake fuskantar sauye-sauyen
tattalin arziki da nufin dawo da daidaito da kuma
ƙarfafa asusun gwamnati.
A cewarsa, tsarin kasafin ya nuna fifikon da aka ba
ayyukan ci gaba, inda aka ware mafi yawan kuɗin
don sassa masu mahimmanci kamar sufuri, wutar
lantarki, noma, ci gaban masana'antu, gidaje, da
fasahar zamani.
Majalisar Dattawa ta kasar nan ta fara muhawara kan lissafin kasafin kuɗin shekarar 2026 da Shugaba
108