Harin ya faru ne da daddare a garin Atoso da ke gundumar Fan ta ƙaramar hukumar Barkin Ladi a lokacin da mutanen ke haƙar ma’adanai bisa ƙa’ida.
Shugaban al’ummar, Solomon Daylop, ya shaida wa BBC cewa waɗanda suka kai harin sun isa wurin ne dayawansu inda suka fara harbi, lamarin da ya jawo firgici da mutuwar mutane da dama. Ya ce tuni aka kai waɗanda suka jikkata asibiti, yayin da mazauna ke cikin baƙin ciki suna kuma shirin yadda za a kuɓuatar da waɗanda akasace.
Hukumar ‘yan sanda ta jihar Plateau ba ta yi wani bayani ba tukuna kan lamarin.
Wannan sabon tashin hankali ya ƙara haifar da fargaba a yankin, inda aka sha fama da hare-hare masu alaƙa da harkokin haƙar ma’adanai da rikice-rikice na dogon lokaci tsakanin manoma da makiyaya. Jihar Plateau ta kasance cibiyar rikici a ‘yan shekarun nan saboda saɓani kan fili da albarkatu da kuma ƙabilanci.
Ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai sun fi mayar da hankali kan wuraren haƙar ma’adanai don samun kuɗi da iko.
A watan Satumba, ma’aikatan ma’adanai huɗu sun mutu a garin Dura sakamakon ruftawar wani wuri haƙar ma’adanai, abin da ke nuna hatsarin wannan aiki da kuma rashin tsaro a yankin.