119
Dokar hana balaguro zuwa Amurka da ta shafi kusan ƙasashe 40 ta fara aiki daga yau 1 ga Janairu.
Fadar White House ta ce ta ɗauki matakin haramcin ne da ya shafi ƙasashen Afrika da dama saboda dalilai na tsaron ƙasa.
Fadar White House ta ce haramcin na balaguro zuwa Amurka ya biyo bayan damuwa kan tsarin tantancewa da kuma matsalar ƴan kama wuri zauna waɗanda ke zarce wa’adin bizarsu.
Sai dai ƙasashen Mali da Burkina Faso da ke ƙarƙashin ikon soji kuma da ke cikin jerin ƙasashen da haramcin ya shafa sun ce su ma za su haramta wa Amurkawa shiga ƙasashensu.
Tuni dai ƙwararru suka ce wannan yunƙuri zai haifar da rashin tabbas ga ‘yan ciranin da yanzu haka ke a Amurka da kuma ƙara tsamin dangantaka tsakanin Amurka da wasu ƙasashe na Afirka.