Hukumar Kare hakkin masu saye da
sayarwa ta tarayya ta bayyana fadada
bincike akan zargin ƙarin kuɗin tikitin jirgin
sama ba bisa ƙa’ida ba da yawancin
kamfanonin jiragen sama na Najeriya su ke
yi.
Rahotanni sun nuna cewa an samu damuwa
game da tsarin da ake amfani da shi wajen
ƙayyade tsadar farashin tikiti da wasu
kamfanonin jiragen sama na cikin gida ke
karɓa a halin yanzu, musamman a kan
hanyoyin zirga-zirgar cikin ƙasa.
Koda a bayabayannan sai da Majalisar
Dattawan Najeriya ta yi tattaunawa mai zurfi
a akan wannan batu, tare da yin kira da a
gudanar da cikakken bincike a kai.
’Yan majalisar sun zargi kamfanonin jiragen
sama na cikin gida da mummunan cin zarafi
ga fasinjoji.
Sun kuma ce ana yawaita samun karuwar
farashin tikitin jirgi a tsakanin kamfanonin
jiragen sama, musamman a lokutan
bukukuwa.
A cewar hukumar, binciken da ake ci gaba
da yi ya shafi kamfanonin jiragen sama da
ke aiki a wasu hanyoyin da aka gano, ciki
har da yankunan Kudu maso Gabas da
Kudu maso Kudu na ƙasar nan.