Shugaban rukunin kamfanonin Dangote Aliko Dangote ne ya bayyana hakan a wajen wani taron menama labarai, inda a ciki ya zargi hukumar da daƙile ayyukan matatun na cikin gida da hana su rawar gaban hantsi ta hanyar yi musu zagon ƙasa, sannan ya zargi hukumar da shugabanta da cin hanci da rashawa.
Dangote ya kuma yi zargin cewa kuɗaɗen da shugaban hukumar Farouk Ahmed ke kashewa sun yi yawa, inda ya ce sun fi ƙarfin abin da ma’aikacin gwamnati yake samu, wanda a cewarsa hakan zai janyo rashin yarda da aminci daga ɓangaren ƴan ƙasa.
BBC ta tuntuɓi kakakin hukumar ta NMDPRA domin jin ta bakinsa kan zargin, amma ya ƙi cewa komai har zuwa lokacin haɗa wannan labarin.
Dangote ya buƙaci hukumar ɗa’ar ma’aikata ko kuma wasu hukumomin gwamnatin ƙasar da suke da alhakin bincike, “da su bincika wannan batun,” in ji shi.
A baya dai hukumar ta zargi matatar man fetur ta Dangote da yunƙurin rufe kowa ta hanyar yin kaka-gida a ɓangaren harkar man fetur, sannan ta ce man da matatar za ta riƙa fitarwa ba zai wadatar da ƴan Najeriya ba.
Najeriya wadda ita ce ta fi kowace ƙasa arzikin man fetur a Afirka, ta daɗe tana fitar da man fetur ɗinta a tace zuwa ƙasaashen waje, sai kuma ta shiga da man.
A ɗaya ɓangaren kuma, matatar Dangote wadda za ta iya tace ganga 650 a kullum, an assasa ta ne domin tacewa da sayar da man fetur a Najeriya a farashin naira.