Gwamnatinmu bazatafadiba dukda tsananin zanga zanga,
Jagoran addinin Iran, Ayatolla Ali Khamenei, ya ce gwamnatin ƙasar ba za ta faɗi ba duk da tsananin zanga-zangar da ake yi a faɗin Iran, wadda aka bayyana a matsayin mafi muni cikin shekaru 15.
Khamenei ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a bainar jama’a karon farko tun bayan ɓarkewar zanga-zangar kusan mako biyu da suka gabata. A jawabin nasa, ya ce gwamnatinsa ba za ta lamunci mutane su riƙa aiki a matsayin sojojin hayar ƙasashen waje ko kuma masu yi wa ƙasashen waje aiki ba.
Dubban mutane ne ke ci gaba da gudanar da zanga-zanga a sassa daban-daban na ƙasar, inda suke kiraye-kirayen tumɓuke gwamnatin Iran, tare da zargin ta da gazawa wajen biyan buƙatun jama’a da kuma take haƙƙoƙinsu.