40
Ma’aikatar Albarkatun Ruwa da Tsabtace Muhalli ta Tarayya ta ware Naira miliyan 140 a cikin kasafin kuɗin shekarar 2026 domin samar da kwamfyutocin tafi-da-gidanka, iPad da wayoyin Android ga matasan mazaɓar Fufore/Song a Jihar Adamawa.
Bayanan kasafin kuɗin, kamar yadda aka bayyana, sun nuna cewa an ware kuɗin ne domin inganta ilimin matasa a fannin fasahar sadarwa da bayanai, wato ICT.
Shirin na daga cikin ayyukan da ma’aikatar ta saka a kasafin kuɗinta na shekarar 2026 domin tallafa wa matasan mazaɓar a fannin fasaha.