Home NewsKotun Ɗaukaka Ƙara Ta Soke Hukuncin Da Ya Rushe Ka’idojin INEC Na Zaɓen 2027

Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Soke Hukuncin Da Ya Rushe Ka’idojin INEC Na Zaɓen 2027

Kotun Ɗaukaka Ƙara ta soke hukuncin wata babbar kotu da ta bayyana ka’idojin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) na gudanar da zaɓen shekarar 2027 a matsayin marasa inganci.

Kotun ta yanke cewa hukuncin da kotun farko ta bayar ba ya da inganci, tare da mayar da cikakken ikon aiwatar da ka’idojin zaɓen 2027 ga Hukumar INEC.

Hakan na nufin ka’idojin da INEC ta fitar domin gudanar da babban zaɓen shekarar 2027 za su ci gaba da aiki har sai an samu wani hukunci na daban daga kotun da ta fi wannan iko ko kuma hukumar ta yi gyara a kansu

You may also like

Leave a Comment