207
Mr Lai wanda ɗan asalin ƙasar Birtaniya ne, ya je kotun domin saurarar shari’ar.
Tuni dai Lai mai kimanin shekaru 78 da haihuwa ya soki hukuncin inda ya bayyana shi a matsayin bita da ƙullin siyasa.
Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗanadam da kuma ƙasashen yamma sun yi allawadai da hukuncin.
Lai shi ne fitaccen mutumin da aka fara tuhuma a ƙarƙashin wata dokar tsaron kasa mai cike da ce-ce-ku-ce wadda China ta ɓullo da ita a 2020.