461
A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta bayyana cewa duk waɗannan rahotanni ba su da tushe balle makama, inda Rundunar ta jaddada cewa jirgin ba ya cikin wani aikin leƙen asiri, kuma ba a tilasta masa sauka ba saboda wani dalili na tsaro ko siyasa.
Rundunar ta bayyana cewa jirgin na kan wani aiki na yau da kullum da aka amince da shi, sai dai ya fuskanci matsala da ta wajabta masa sauka a kasar ta Burkina Faso domin kare lafiyar jirgin da ma’aikatan da ke cikinsa.
Rundunar ta ƙara da cewa Najeriya na mutunta ikon ƙasashe makwabta, tare da bin ƙa’idojin hulɗar ƙasa da ƙasa, kuma ba za ta taɓa amfani da jiragen sojanta wajen tsoma baki ko leƙen asiri a kan wata ƙasa ba.