Home NewsShugaban Kasa Bola Tinubu ya yi kira ga gwamnoni da ‘Yayan Jam’iyyar APC da sauran gwamnoni da su mara baya ga bukatar kafa ‘Yan sandan jahohi tare da tabbatar da ‘Yancin kananan hukumomi.

Shugaban Kasa Bola Tinubu ya yi kira ga gwamnoni da ‘Yayan Jam’iyyar APC da sauran gwamnoni da su mara baya ga bukatar kafa ‘Yan sandan jahohi tare da tabbatar da ‘Yancin kananan hukumomi.

Shugaban Kasa Bola Tinubu ya yi kira ga gwamnoni da ‘Yayan Jam’iyyar APC da sauran gwamnoni da su mara baya ga bukatar kafa ‘Yan sandan jahohi tare da tabbatar da ‘Yancin kananan hukumomi.

Tinubu ya bayyana hakanne ayayin taron Kwamitin Dattawa na Jam’iyyar APC na Kasa karo na 14 da ya gudana a Abuja.

Ya kuma roƙi gwamnonin jihohi da su goyi bayan hukuncin Kotun Ƙoli game da ‘yancin cin gashin kai na ƙananan hukumomi.

A cewarsa, ba wai kawai kotu ta yanke hukunci ba ne ya isa; dole ne kuɗaɗen rabon da ake ware wa ƙananan hukumomi su riƙa isa gare su kai tsaye.

Haka kuma, Shugaba Tinubu ya yi kira da a ƙara bai wa mata dama a kwamitin Dattawa na kasa na Jam’iyyar APC domin tabbatar da daidaito a tsakanin maza da mata.

You may also like

Leave a Comment