Tinubu wanda mataimakin shugaban Kasa Kashim Shettima ya wakilta ya bayyana hakanne ayayin taron kwanaki biyar na babban Rundunar Sojin Nigeria na shekarar 2025 wanda ya gudana a jahar legos.
Taken taron shi ne “ sake nazartar aiyukan ta’addanci da madubin diflomasiyya da kuma karfin soji”.
Da ya ke bayyana bude taron shugaban Kasa Bola Tinubu ya ce ya na sane da irin sadaukarwar da Dakarun Sojin Nigeria su ke nunawa a fadin Kasar nan.
A cewarsa Dakarun Sojin Kasar nan su na bin Nigeria bashin da ba za a iya bayyana girmansa ba da fatar baki a saboda yadda Dakarun su ka zabarwa kansu yin aiki tukuru ga kasa a maimakon Jindadinsu, da yadda su ke tunkarar kalubalen tsaro domin al’ummar Nigeria su iya yin Bacci a cikin kwanciyar hankali da nutsuwa.
Hakanan shugaban Kasa ya jaddada Kudirin gwamnatin tarayya na cigaba da tallafawa Rundunar Sojin Kasar nan domin ta cigaba da sauke nauyin da Kundin tsarin mulkin kasa ya dora mata.