Rasha ta sake kai wasu manyan hare-hare da jirgin sama maras matuki da kuma na makami mai linzami a kan biranen Ukraine.
Hukumomin Ukraine sun ce aƙalla mutum huɗu sun rasa rayukansu a birnin Kharkiv da ke gabashin ƙasar.
Rahotanni sun kuma ce an ji fashe-fashe a babban birnin ƙasar, Kyiv, lamarin da ya tayar da hankula a tsakanin mazauna birnin.
Hare-haren sun sake janyo cikas ga rayuwar jama’a, musamman wajen samar da wutar lantarki da makamashin dumama waje.
Ma’aikata na ƙoƙarin dawo da wutar lantarki da hanyoyin samar da makamashi, tun bayan harin da Rasha ta kai kan muhimman kayayyakin samar da makamashi a makon da ya gabata.
A ɗaya ɓangaren kuma, Rasha ta ce Ukraine ta kai mata hari a birnin Taganrog da ke kudancin ƙasar, inda rahotannin da ba a tabbatar ba ke nuna cewa an kai harin ne kan wata masana’antar ƙera jiragen sama marasa matuƙa. do a headline for this