Home NewsMa’aikatar Albarkatun Ruwa Ta Ware Naira Miliyan 140 Domin Samar wa Matasan Adamawa Kwamfutoci da Wayoyin Hannu

Ma’aikatar Albarkatun Ruwa Ta Ware Naira Miliyan 140 Domin Samar wa Matasan Adamawa Kwamfutoci da Wayoyin Hannu

Ma’aikatar Albarkatun Ruwa da Tsabtace Muhalli ta Tarayya ta ware Naira miliyan 140 a cikin kasafin kuɗin shekarar 2026 domin samar da kwamfyutocin tafi-da-gidanka, iPad da wayoyin Android ga matasan mazaɓar Fufore/Song a Jihar Adamawa.

Bayanan kasafin kuɗin, kamar yadda aka bayyana, sun nuna cewa an ware kuɗin ne domin inganta ilimin matasa a fannin fasahar sadarwa da bayanai, wato ICT.

Shirin na daga cikin ayyukan da ma’aikatar ta saka a kasafin kuɗinta na shekarar 2026 domin tallafa wa matasan mazaɓar a fannin fasaha.

You may also like

Leave a Comment