Rundunar ‘Yan Sandan jihar Katsina ta ce ta daƙile wasu hare-hare biyu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai a ƙananan hukumomin Kankia da Charanchi, inda ta ceto mata biyu da aka yi garkuwa da su ba tare da sun samu wani rauni ba.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Abubakar Sadiq-Aliyu, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.
Ya ce lamarin farko ya faru ne a ranar Asabar da misalin ƙarfe 11:45 na safe, lokacin da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne, ɗauke da makamai a kan babura uku suka kai hari ƙauyen Jauga da ke Sabon Gida a ƙaramar hukumar Kankia, inda suka yi garkuwa da mata biyu.
A cewarsa, da samun rahoton harin, jami’in ‘yan sanda mai kula da shiyyar Kankia (DPO) ya jagoranci tawagar jami’ai zuwa wurin da abin ya faru cikin gaggawa.
Ya ce jami’an sun fafata da maharan a musayar wuta, lamarin da ya tilasta musu tserewa cikin daji tare da samun raunukan harbin bindiga wanda ya tilasta musu barin matan da suka sace.
Waɗanda aka ceto sun haɗa da Rukayya Yahaya mai shekara 20 da Sahura Abdulhadi mai shekara 22, da ke zaune a yankin.
A wani samame na daban, kakakin rundunar ya ce a ranar Litinin da misalin ƙarfe 10 na safe, rundunar ta kuma dakile yunƙurin satar shanu a ƙauyen Majen Waya da ke ƙaramar hukumar Charanchi.
Ya bayyana cewa wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kutsa cikin ƙauyen da nufin sace shanu, amma jami’an ‘yan sanda sun kai ɗauki cikin gaggawa.
A cewarsa, DPO na Charanchi ya tura tawagar sintiri tare da motar yaƙi mai sulke (APC), inda suka yi musayar wuta da maharan.